Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24- ta rawaito Abbas Musawi ya na cewa, tekun da yake a yammacin kasar Iran sunansa tekun fasha, kamar yadda hakan yake rubuce a cikin dukkanin kundaye na kasa da kasa.
Wannan martani dai na zuwa ne bayan da shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, ya aike da dakaru zuwa yankin tekun arab da fasha.
Abbas Musawi ya ce bai kamata a saka siyasa a cikin lamurra da suke tabbatattu a cikin tarihin duniya ba, musamman lamurra da majalisar dinkin duniya ta tabbatar da su a hukumance.